<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>65</hymn_number>
<title>Don Jibin Nan, Mai Fansarmu LW65</title>
<lyrics>[V1]
 1) Don jibin nan, Mai Fansarmu,
 Gurasarka da ƙoƙonka,
 Ƙaunarka da alherinka,
 Mun gode maka, Yesunmu.

[V2]
 2)  Kai ne ka ɗauke laifinmu,
 Ka wanke mu da jininka,
 Kai ne ka zama gurbinmu,
 Mun gode maka, Yesunmu.

[V3]
 3) Domin ka ɗauki giciyenka,
 Ka kuma raina kunyarsa
 Domin ka ba da jininka,
 Mun gode maka, Yesunmu.

[V4]
 4) Domin ka aiko Ruhunka,
 Shi koya mana nufinka,
 Shi buɗe mana kalmarka,
 Mun gode maka, Yesunmu.

[V5]
 5) Domin alkawarinka fa
 Na shirin zaman masu bi
 Har za ka zo ka karƃe mu,
 Mun gode maka, Yesunmu.</lyrics>
</song>